IQNA

Daukaka Na Tare Da Yin Riko Da Kur'ani

23:49 - April 24, 2018
Lambar Labari: 3482599
Bangaren kasa da kasa, Iyas said wani mahardacin kur'ani mai tsarki daga kasar Zimbabwe da ke halartar gasar kur'ani ya bayyana kur'ani a matsayin tushen dauaka.

 

A zantawar da ya yi da kamfanin dillancin labaran iqna Ilyas Said makaranci kuma mahardacin kur'ani mai tsarki da ke halrtar gasar kur'ani ta duniya da ke gudana a Iran, ya bayyana kur'ania  matsayin tushen duk wata daukaka ta dana dam.

Ya ce tun yana karami yana da shawar kartun kur'ani mai tsarki, duk kuwa da cewa ya tashi ya ga mahaifansa suna yin karatun kur'ani kuma hakan yana burge shi.

Ilyas ya ce ko shakka babu mahaifansa sun taka gagarumar rawa wajen kwadaitar da shi dangane da lamarin kur'ani, kuma tun daga lokacin da ya samu karfin gwiwa daga mahaifansa, ya ci gaba da bayar da himma kan lamarin kur'ani mai tsarki.

Dangane da yanayin kasar ta Zimbabwe ya bayyana cewa ba kasa ce ta musulmi ba, amma kuma duk da haka suna zaune da juna lafiya, suna girmama juna tsakaninsu da sauran mabiya addinai, musamman ma kiristoci wadanda su ne suka fi yawa a kasar.

Amma duk da haka akwai cibiyoyi na musulmi wadanda ake koyar da karatun addini da suka hada har da kur'ani, wadanda suke bayar da gagarumar gudunmawa wajen ilmantar da musulmi, wanda shi ma ya amfana da su matuka a wajen karfafa hardarsa da karatunsa.

3708509

 

 

captcha