IQNA

Makaho Dan Najeriya Da Ya Iya Karatu Tare Da Hardace Kur’ani Cikin Shekara Daya

23:34 - April 25, 2018
Lambar Labari: 3482602
Bangaren kasa da kasa, Ali Idris Abdulsalam dan shekaru 35 wani mai larurar gani ne dan Najeriya, wanda ya iya karatun kur’ani tare da hardace shi cikin shekara daya, wanda kuma yake halartar gasar kur'ani ta duniya yanzu haka a Tehran.

 

Idris wanda dan jahar Kano ne a tarayyar Najeriya, a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa, ya kasance an haife shi ba tare da wata matsalar idanu ba, amma sakamakon kamuwa da wata rashin lafiya ya rasa ganinsa a cikin shekara ta 1995.

Ya ce ya fara koyon karatun kur’ani gadan-gadan da kuma harda, a lokacin yana da shekaru goma sha uku da haihuwa, a lokacin da ya cika shekaru 14 da haihuwa ya kammala koyon karatu bisa kaida da sanin hukunce-hukunce, da kuma hardace kur’ani baii daya a cikin shekara.

Ya kara da cewa bisa tsari na al’adar hausawa, yaro idan ya tashi tun yana karami yake fara koyon karatun kur’ani, kuma a lokacin da zai girma ko da ya yi nisa ne a cikin boko amma dai ya san wani abu na kur’ani.

Haka nan kuma ya yi ishara da irin rawar da mahaifansa suka taka wajen taimaka masa domin ganin ya cimma wannan buri.

Kamar yadda kuma ya bayyana Malam Ahmad Haruna a matsayin malaminsa na farko na kur’ani, sai kuma Malam Salisu da Malam Haruna Bashir a matsayi na biyu.

Ya ce yanzu haka yana koyarwa a wata daya daga cikin jami’oin Najeriya, inda yake koyar da makafi a bangaren ilimin kur’ani.

3708544

 

 

 

captcha