IQNA

Bude Cibiyar Binke Kan Ilmomin Muslunci A Jami’ar Zimbabwe

23:41 - April 25, 2018
Lambar Labari: 3482604
Bangaren kasa da kasa, a ganawar da aka yi da Iyai Mowati da shuban karamin ofishin jakadancin Iran a Zimbabwe an tattauna batun bude cibiyar bincike ta musulunci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa a ganawar da aka yi tsakanin Reza Askari da kuma shugaban jami’an Zimbabwe, an tattauna ne kan hanyoyi kara bunkasa bincike na ilimi, inda suka cimma matsaya kan bude wata cibiya ta bincike kan ilmomin muslunci.

Karamin jakadan an Iran ya ce za su dauki nauyin aikin gina wannan cibiya, wadda za ta ita ce ta farko a wannan jami’a, wadda za ta zama mai amfani ga dukaknin masu bincike kan addinin muslunci a wannan jami’a.

Shi ma a nasa bangaren shugaban jami’ar ta Zimbabwe ya bayyana farin cikinsa matuka dangane da yadda wannan ganawa ta kasance, da kuma abubuwan da suka cimmawa, wanda idan aka aiwatar da su za a amfana matuka.

Ya ce ko shakka babu kasashen Iran da Zimbabwe suna dadadiyar alaka da siyasa da ilimi da kasuwanci da sauransu, weanda kuma wannan zai zama ci gaba ne na wanann alaka da kuma kara fadada ta.

Bangarorin biyu sun cimma matsa kan gudanar da wani taro nan ba da jimawa ba wanda zai hada dukkanin bangarori ma’aikatun ilimi na kasashen biyu, domin fara aiwatar da wananns hiri.

3708999

 

 

 

captcha