IQNA

Bayar Da Buda Baki Ga Matasa Musulmi A Sweden

23:45 - May 19, 2018
Lambar Labari: 3482672
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Stockholm na kasar Sweden ta shirya wa matasa musulmi buda baki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Stockholm na kasar Sweden ta shirya buda baki ga matasa musulmi masu azumi.

Dukkanin matasan da aka gayyata shkarunsu na tsakanin 15 zuwa 20, wadanda za su yi buda baki a yau 19 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2018 da muke ciki.

Bayan kammala buda bakin za a gabatar da jawabi ga matasan kan muhimman lamurra da suka shafi zamantakewarsu a cikin al’umma, musamman dai su da suke rayuwa a cikin wani yanayi mai wahalar gaske ta fuskar tarbiyar musulunci.

3715579

 

 

captcha