IQNA

Gasar Kur’ani Ta Watan Ramadan A Kasar Ghana

23:54 - June 01, 2018
Lambar Labari: 3482715
Bangaren kasa da kasa, an bude gasar kur’ani mai tsarki ta watan Ramadan a birnin Akra na kasar Ghana.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an bude gasar kur’ani mai tsarki ta watan Ramadan a birnin Akra na kasar Ghana a jiya Alhamis.

Gasar dai ana gudanar da ita ne a bangarorin hardar dukkanin kur’ani da kuma hardar rabin kur’ani sai kuma hardar ihizi goma sha biyar.

Cibiyar Nur ce dai take daukar nauyin shiryawa da gudanar da wannan gasa a kowace shekara a cikin watan azumin ramadana.

An kafa kungiyar ne dai tun a cikin shekara ta 2003, inda wasu daga cikin daliban jami’a musulmi suka hadu suka kafa kungiyar da nufin yada koyarwar musulunci.

Kasar Ghana dai tana daga cikin manyan kasashen yammacin nahiyar Afirka, kuma kimanin kashi 45 cikin dari na mutanen kasar musulmi ne.

3719353

 

 

 

 

 

 

 

captcha