IQNA

Wakilin Iran Zai Shiga Gasar Kur’ani Ta Duniya A Aljeriya Da Za A Fara A Yau

23:37 - June 05, 2018
Lambar Labari: 3482730
Bangaren kasa da kasa wakilin kasar Iran ya samu damar shiga cikin wadanda za su shiga gasar kur’ani ta duniyaa Aljeriya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Muhammad Mahmudi, wakilin kasar Iran ya samu damar shiga cikin wadanda za su shiga gasar kur’ani ta duniya a kasar Aljeriya da za a fara gudanawa a daren yau.

Bayanin ya ce a yau ne aka kammala tantance dukkanin wadada suka zo daga kasashen duniya, domin fitar da wadanda za su iya shiga gasar, ta hanyar amsa wasu tambayoyi.

Muhammad Mahmudi ya samu damar amsa dukkanin tambayoyin da alkalan gasar suka yi masa, nda suka ba shi damar shiga gasar ba tare da wani shamaki ba.

Wannan mahardacin kur’ani dan kasar Iran mai shekaru 17 da haihuwa, ya wakilci kasar a wasu tarukan gasar kur’ani na duniya, na baya-bayan nan shi ne gasar kur’ani ta duniya a Kuwait.

3720549

 

 

 

 

 

captcha