IQNA

Mahardata 1200 A Gasar Kur’ani Ta Alkahira

22:41 - June 07, 2018
Lambar Labari: 3482736
Bangaren kasa da kasa, mahardata kur’ani mai tsarki su 1200 n za su halarci gasar kur’ani ta birnin Alkahira a Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau ne za a fara gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki ta birnin Alkahira da ake gudanarwa a kowace shekara.

Atef Abdulhamid gwamnan Alkahira da kuma Muhamad Sayyid shugaban bangaren kula da harkokin addini na birnin da wasu manyan jami’ai daga ma’aikatu daban-daban duk za su halarci taron bude gasar a daren yau Alhamis.

Muhammad Sayyid ya ce adadin wadanda suka yi rijistar halartar gasa ya kai mahardata 1200.

Ya kara da cewa, za a gudanar da gasar kamar yadda aka saba a dukkanin bangarori na harda, haka nan kuma daga karshe za a bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo.

3720823

 

 

 

 

 

captcha