IQNA

Sakon Ranar Quds Daga Al’ummar Teran Zuwa Ga Al’ummar Palastine

23:55 - June 08, 2018
Lambar Labari: 3482739
Bangaren siyasa, Tun da safiyar yau ne 23 ga Ramadan 1439 miliyoyin al'ummar Iran, maza da mata suka fito kan titunan kusan dukkanin garuruwan kasar don amsa kiran marigayi Imam da kuma raya Ranar Kudus ta duniya don sake jaddada goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da ake zalunta.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna, rahotanni daga bangarori daban-daban na kasar musamman a birnin Tehran, babban birnin kasar ta Iran, sun bayyana dubun dubatan al'ummar birnin ne da suka hada da manyan jami'an gwamnati, jami'an sojoji da na 'yan sanda, manyan malamai da sauran al'umma ne suka fito don nuna goyon bayan su ga al'ummar Palastinu da kuma yin Allah wadai da yahudawan sahyoniya da masu goya musu baya musamman Amurka da 'yan amshin shatansu.

Masu zanga-zangar dai suna rera take da kuma rike da kwalaye da tutoci da suke nuna yin Allah wadai dinsu da haramtacciyar kasar Isra'ila, Amurka da wasu shugabannin kasashen larabawa da suke hada kai da su wajen cutar al'ummar Palastinu.

Kimanin shekaru talatin da tara kenan marigayi Imam Khumaini ya  sanya ranar juma'ar karshe ta watan Ramalana a matsayin Ranar Kudus ta duniya don nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu yana mai kiran al'ummar musulmi da su girmama wannan ranar.

Mahalarta jerin gwanon Ranar Kudus ta duniya da aka gudanar a Tehran da sauran garuruwan Iran sun jaddada wajibcin 'yanto masallacin Kudus daga mamayar sahyoniyawa da kuma kokari wajen ganin bayan haramtacciyar kasar Isra'ila.

Masu jerin gwanon sun bayyana hakan ne cikin sanarwar bayan taron da suka fitar a yau din nan jim kadan bayan kammala jerin gwanon ranar Kudus din da aka gudanar a nan Tehran, inda yayin da suke yin Allah wadai da mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Kudus da shugaban Amurka yayi da kuma bayyanar da birnin na Kudus a matsayin babban birnin HKI, suna bayyana cewa birnin Kudus shi ne babban birnin kasar Palastinu, kuma ya zama wajibi musulmi su yi kokari wajen 'yanto birnin daga mamayar sahyoniyawa.

Har ila yau masu jerin gwanon sun yi Allah wadai da makircin da Amurka da wasu kasashen larabawa suke kulla wa al'ummar Palastinu na yin sulhu da sahyoniyawa a abin da suka kira shi da  yarjejeniyar karni, inda suka ce hanya guda kawai ta 'yanto Palastinu shi ne barin Palastinawa su dawo kasar su sannan a gudanar da kuri'ar jin ra'ayinsu don su zaba wa kansu abin da suke so da kansu.

Har ila yau masu jerin gwanon sun bayyana shan kashin da kungiyar ta'addancin nan ta Daesh ta sha a kasashen Siriya da Iraki da kuma gazawar da Saudiyya ta yi wajen cimma bakar aniyarta a kan al'ummar Yemen da Bahrain a matsayin babbar nasara, suna masu cewa al'ummar musulmi ba za su taba bari makiyansu su cimma bakar aniyarsu a kansu ba. 

3718729

 

 

 

 

 

captcha