IQNA

Iran Ta Shirya Wa Musulmin Rasha Buda Baki

23:47 - June 10, 2018
Lambar Labari: 3482745
Bangaren kasa da kasa, kasar Iran ta dauki nauyin shiryawa musulmin kasar Rasha wani buda baki a birnin Moscow fadar mulkin kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an shirya wannan buda baki ne a masallacin Memorial da ke cikin birnin Moscow.

Hojjatol Islam Akbar Jaddi shi ne wakilin jagora a kasar Rasha, wanda kuma ya kasance daga cikin masu jawabi.

Shi ma a nasa bangaren Ahmad Hadariyan mataimakin jakadan Iran a kasar Rasha, ya gabatar da jawabi, inda ya isar a sakon ‘yan uwantaka na al’ummar Iran ga musulmin Rasha.

Ya ce o shakka babu akwai dadadden tarihi kasashen biyu, kuma ta fuskar siyasa gwamnatocin Iran da Rasha suna da kyakkyawar dangantaka.

3721325

 

 

ضیافت افطار ایران در روسیه+عکس

ضیافت افطار ایران در روسیه+عکس

ضیافت افطار ایران در روسیه+عکس

ضیافت افطار ایران در روسیه+عکس

ضیافت افطار ایران در روسیه+عکس

 

captcha