IQNA

A Yau Ne A Kasar Mauritania Za A Bude gasar Kur’ani Ta Kasa Da Kasa

23:15 - June 11, 2018
Lambar Labari: 3482747
Bangaren kasa da kasa, a yau ne za a bude babbar gasar kur’ani ta kasa da kasa a binin Nuwakshout na kasar Mauritania.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau ne za a bude babbar gasar kur’ani ta kasa da kasa a binin Nuwakshout na kasar Mauritania.

Wannan gasar dai ana yi mata lakabi ne da gasar kyauta ta shugaba Muhammad Wuld Abdulaziz shugaban kasar ta Mauritania.

Ana gudanar da gasar ne a kowane watan azumin Ramadan kuma wannan shi ne karo na uku a jere an gudanar da ita, inda shugaban kasar ta Mauritania Muhammad Wuld Abdulazizi ne da kansa yake daukar nauyin gasar.

Daga cikin kasashen da ke halartar gasar akwai Aljeriya, Moroco, Tunisia, Libya da kanta Mauritania.

Haka nan kuma akwai wasu daga cikin kasashe masu makwabtaka da kasar da suka turo nasu wailan.

3721890

 

 

captcha