Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya fiye da mutane miliyan biyu nesuka halaci sallar daren ashirin da bakawai ga watan Ramadan da zimmar riskar daren lailatul qadr a birnin masallacin harami mai alfarma.
Masu aikin Umrah daga sassan duniya ne suka cika masalacin harai mai alfarma na Ka’abah a daren na jiya domin samun falalar daren da wasu ‘yan sunna suke ganin yafi kusa da zama daren lailatul qadr.
Haka lamarin yakea masallacin manzon Allah (ASW) a birnin Madina, inda a can dubban daruruwan masallata ne suka aru domin yin ibada a wannan dare.
A masallacin quds kuma duk da matakan da yahudawan Isra’ila suka dauka na kayyade adadin mutane masu shiga masallacin mai alfarma, fiye da mutane dubu 350 n suka gudanar da salar.
Yahudawan sahyuniya sun kayyade shekarun masallacin da cewa kada ska zama kasa da 40, amma duk da haka an cika masallacin makil.