IQNA

Shugaba Rauhani Ya Aike Da Sakonnin Taya Murnan Sallah Ga Shugannin Kasashen Musulmi

23:53 - June 14, 2018
Lambar Labari: 3482756
Bangaren kasa da kasa, shugaba Rauhani na Iran ya aike da sakonnin taya murnar kammala azumin watan ramadan zuwa ga shugabannin kasashen musulmi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin sakon nasa, shugaba Rauhani ya bayyana farin cikinsa da Allah ya nuna mana karshen azumin watan Ramadan lafiya a wannan shekara, tare da yin fatan Alah ya karbi dukkanin ayyukan ibada na al’ummar musulmi baki daya.

Haka nan kuma Rauhani ya yi wasauran takwarorinsa na kasashen musulmi fatan za a yi bukukuwan salla lafiya, tare da yin fatan hakan ya zama wani mabudi na alkhairi ga al’ummominsu da sauran dukkanin kasashen musulmi baki daya.

Kamar yadda ya yi fatan Allah ya kawo al’ummar musulmi zaman lafiya da wanciyar hankali, ya kuma fadakar da shugabannin musulmi kan wajabcin sauke nauyin da ke kansu na tabbatar da samar da hadin kan al’ummar musulmi da kaucewa hankoron masu son ganin sun kawo Baraka tsakanin al’ummar domin su shagaltar da musulmi da kawukansu.

3722896

 

 

 

 

captcha