Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Wasu mahara sun kai farmaki cikin wani Masallaci a garin Malmezebury da ke kusa da jihar Cape Town a shiyar kudu maso yammacin kasar Afrika ta Kudu, inda suka soke mutane biyu da wuka har lahira tare da jikkata wasu adadi masu yawa.
Jami'an 'yan sandan Afrika ta Kudu sun samu nasarar hanzarta kawo dauki Masallacin, inda suka harbe maharan biyu har lahira. Rundunar 'yan sandan jihar Cape Town ta fara gudanar da bincike domin gano dalilin maharan na kai hari cikin Masallacin.