IQNA

An Wanke Sheikh Ali Salman Daga Tuhumce-Tuhumcen Da Ake Yi Masa

23:54 - June 21, 2018
Lambar Labari: 3482775
Bangaen kasa da kasa, kotun kasar Bahrain ta tabbatar da cewa zargin da ake yi wa shugaban jma’iyar Wifaq a kasar Sheikh Ali Salman da Hasan Sultan Ali Aswad ba gaskiya ba ne.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin tashar alalam ya bayar da rahoton cewa, kotun kasar Bahrain ta tabbatar da cewa zargin da ake yi wa Sheikh Ali Salman da Hasan Sultan Ali Aswad kan yi wa Qatar liken asiri bah aka lamarin yake ba.

Kotun ta tababtar da hakan ne bayan kasa tabbatar da wasu dalilai kan hakan, kamar yadda kuma binciken da ta gudanar ya nuna sabanin haka.

Baya gahaka kuma a cikin makon nan kimanin kungiyar kare hakkin bil adama na duniya talatin da biyar ne daga kasashe ashirin da biyar suka bukaci masarautar Bahrain da ta gagaguta sakin Sheikh Ali Salman ba tare da wani sharadi ba.

Yanzu haka dai sheikh Ali Salman yana cikin shekara ta hudu a tsare a gidan kaso masarautar kama karya ta Bahrain.

3724340

 

 

 

 

 

captcha