IQNA

Mai Tarjamar Kur’ani A Cikin Harshen Ubek Ya Rasu

23:29 - July 01, 2018
Lambar Labari: 3482800
Bangaren kasa da kasa, Anwar Tursunov mai tarjamar kur’ani dan kasar Uzbekistan ya rasu yana da shekaru 60.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mutum na farko da ya tarjama kur’ani a cikin harshen Uzbek Anwar Tusunov ya rasu.

An haife shi a shekarar 1958, yay i karatun adabi a jami’ar Tashkand, inda ya kammala karatunsa a shekarar 1981.

Ya kasance shi ne babban editan mujallar matasa ta kasar Uzbeistan, daga bisani kuma ya ci gaba da ayyukan koyarwa  ajami’a.

A cikin shekara ta 1994, an nada shi a matsayin limami mai huduba masallaci Tashkand babban birnin kasar Uzbekistan, jama’a da dama sun san shi a matsayin wani mutum mai himma wajen yada lamarin addinin musulunci.

3726647

 

 

 

 

 

captcha