IQNA

Rouhani: Muna Son Alaka Ta Adalci Da Sulhu Tare Da Kasashen Duniya

23:52 - July 03, 2018
Lambar Labari: 3482803
Bangaren kasa da kasa, Rouhani ya bayyana hakan ne a daren jiya lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taron karramawa da aka shirya masa a birnin Genneva na kasar Switzerland.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yayin jawabin nasa, Rouhani ya ci gaba da cewa, ko shakka babu Iran tana girmama sauran kasashen duniya, kuma dole ne duk wata alaka ta kasa da kasa ta zama bisa girmama juna domin amfanin dukkanin bangarori.

Dangane da ficewar Amurka daga yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya kuwa, Rouhani cewa ya yi, dukkanin kasashen duniya sun tabbatar da cewa Iran tana mutunta wannan yarjejinya kuma tana yin aiki da ita kamar yadda aka rattaba hannu a kanta, saboda haka a nan kowa ya san wane ne ya saba wa ka’ida ta kasa da kasa tsakanin Amurka da Iran.

Dangane da matsin lamabar da Amurka take yi wa Iran kuwa ta fuskar tattalin arziki, Rouhani ya ce matsin lamba ba zai iya tilasta Iran ta saba wa ka’ida ko yin abin da ya saba wa maslahar al’ummarta ba.

3727353

 

 

 

captcha