IQNA

Taron Koli Na Kwamitin Kasashen Musulmi A Masar

22:05 - July 10, 2018
Lambar Labari: 3482821
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron koli na kwamitin kasashen musulmi karo na ashirin da tara a birnin Alkahira na kasar Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, nan da watanni biyu masu zuwa za a gudanar da taron koli na kwamitin kasashen musulmi karo na ashirin da tara a birnin Alkahira.

M'ikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa an cimma matsaya kan gudanar da taron a birnin alkahira a cikin watan satumba mai zuwa, wanda zai samu halartar baki daga kasashen musulmi.

Babbar manufar taron dai ita ce bijiro da muhimman lamurra da suke ciwa al'ummar musulmi tuwo a kwarya da kuma gabatar da hanyoyin warware su, ta hanyoyi na ilimi da hankali ba ta hanyar yaki da kashe-kashe ba.

Kimanin kasashe 40 ne dai za su halarci zaman taron, haka nan kuma za a gabatar da shwarwari wadanda za a yi dubia  kansu kafin zaman a gaba.

3728902

 

 

 

captcha