IQNA

Sojojin Ruwa Na Libya Sun Tseratar Da 'Yan Ci-Rani 104 Daga Nutsewa

23:49 - July 13, 2018
Lambar Labari: 3482834
Bangaren kasa da kasa, Jami'an sojin ruwa na kasar Libya sun tseratar da wasu 'yan ci-rani 104 daga nutsewa cikin tekun mediterranean.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, jami'an sojin ruwan na Libya sun hango mutanen ne a cikin kwale-kwale na balon-balon a lokacin da igiyar ruwa take kada su, inda suka kai musu daukin gaggawa tare da tseratar da su daga nutsewa.

Dukkanin mutanen da suke cikin kwale-kwalen dai sun tsira, kuma an nufi da su yankin Alkhams da ke kusa da birnin Tripoli, kuma mutanen sun fito ne daga kasashen Masar, Tunisia, Sudan da kuma Morocco, inda suke nufin tsallakawa zuwa nahiyar turai ta barauniyar hanya.

Masu shiga nahiyar turai ta baraunaiyar hanya domin ci rani suna yin amfani da hanyoyin ruwa na kasar Libya domin tsallakawa nahiyar turai, inda wasu kan nutse a cikin ruwa, wasu sukan isa amma kuma su kan fada hannun jami'an tsaro na kasashen turai.

3729543

 

 

captcha