Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an samar da makarantu 10 na hardar kur’ani mai tsarki a gundumar Aqsar da ke Masar a cikin ‘yan makonnin baya-bayan nan.
Babban daraktn kula da harkokin addini na yankin ya bayyana cewa, sama da wadannan makaratu yana da matykar muhimmanci wajen kara karfafa ayyukan kur’ani a yankin.
Yankunan sun hada da Asna, Tud, Armanat, Zainiya, Qurnah , Asfun, dukkansu suna cikin gundumar Aqsar.