IQNA

Isra’ila Ta Hana Masu Kare Hakkokin Dan Adam Shiga Palatine

23:35 - July 31, 2018
Lambar Labari: 3482848
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta hana wasu rajin kare hakkokin bil adama shiga Palastine.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da hana duniya sanin hakikanin abin da yake faruwa a cikin yankunan Falastinawa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta hana wasu rajin kare hakkokin bil adama shiga Palastine da suka fito daga kasashen duniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wadannan masu fafutuka suna kokarin ganin sun samu cikakken bayani kana bin da yake faruwa na zalunci da danniya da al’ummar Palastine suke fuskanta daga yahudawan sahyuniya.

Daga masu fafutukar akwai wanda aka tsare a filin sauka da tashin jiragen sama na bin Goriyo na tsawon sa’oi ashirin da hudu, a lokacin da yke shirin zuwa tarbar Ahed Tamimi da aka sake ta daga gidan kaso.

3734697

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha