Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake shirin fara ayyukan hajjin bana, an gudanar da wani shiri na bayar da horo kan yadda ake yin mu’amala da alhazai a masallacin annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa a birnin Madina ma alfarma.
Babbar manufar shirin da ita ce koyar da ma’aikata a masallatai sanin yadda za su yi mu’amala da baki da suka fito daga kasashen duniya domin sauke farali.
Sulaiman Abdullah bin Abdullah Rumi ya bayyana cewa, aiwatar da wannans hiri yana da matukar amfani, domin hakan zai kara kare mutuncin kasar da ke daukar bakuncin taron na hajji.