IQNA

Aljeriya Da Indonesia Sun Rattaba Hannu Kan Yin Aiki Tare

23:15 - August 18, 2018
Lambar Labari: 3482902
Bangaren kasa da kasa, kasashen Aljeriya da Indonesia sun rattaba hannu kan yarjejeniyar yin aiki tare da wajen yada sahihiyar fahimta ta zaman lafiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne kasashen Aljeriya da Indonesia sun rattaba hannu kan yarjejeniyar yin aiki tare da wajen yada sahihiyar fahimtar ta zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Tawagar kasar Aljeriya da ta isa kasar Indonesia tare da halartar manyan jami'ai daga ma'aikatun addini da yada al'adu na kasashen biyus un gudanar da tattaunawa.

Dukkanin bangarorin biyu sun rattaba hannu hannu kan yarjejeniyar yin aiki tare domin kara wayar da kan al'ummominsu domin yada zaman lafiya da fahimtar juna, da kuma yin aiki da matsakaicin ra'ayi a kowane lokaci, maimakon tsatsauran ra'ayi a cikin lamarin addini da zamantakewa.

 3739150

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha