Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau Lahadi maniyyatan suna fita daga birnin Makka zuwa Mina inda za su raya ranar “tarwiyyah’ gabanin wuce wa zuwa filin Arfaha a gobe Litinin inda za yi tsayuwar Arfaha da take a matsayin rukuni mafi girma na aikin Haji.
A gefe daya ma’aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ta sanar da cewa adadin maniyata da su ka isa kasar sun kai miliyan biyu.
Bugu da kari mahukuntan Saudiyyar sun sanar da kammala dukkanin shirye-shirye domin gudanar da aikin haji na bana.
Hajjin an bana dai yana daga cikin makamantansa ad suka gabata a cikin ‘yan shekarin nan da ke fuskantar kayyade maniyyata daga kasashen duniya daga bangaren masu rike da madafun iko a kasar Saudiyyah.