Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Abdulaziz Najjar shugaban hukumar zartarwa ta lardin fayum, ya jagoranci girmama wasu daliban kur'ani mahardata su 174 a lardin na Fyum.
Dukkanin daliban dai sun hardace kur'ani mai tsarki kuma sun kasance daga cikin masu nuna kwazo matuka a makarantunsu.
An gudanar da taron girmama daliban ne a babban dakin gudanar da taruka na lardin Fayuma jiya, inda aka basu kyautuka da kuma allunan yabo.