Kakakin cibiyar kula da ayyukan jin kai a fannin kiwon lafiya a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya Isamah Ali ya bayyana cewa,dauki ba dadi tsakanin kungiyoyin da suke dauke da makamai a birnin Tripoli fadar mulkin Libiya da kuma gefen kudancin birnin kasar a cikin mako guda kacal ya lashe rayukan mutane tare da jikkata wasu 159 na daban, baya ga tilastawa iyalai da dama tserewa daga muhallinsu.
A gefe guda kuma majiyoyin watsa labaran Libiya sun sanar da cewa, a cikin 'yan watannin nan an sace matan aure sha daya da budurwaye ashirin da daya a yankuna daban daban na kasar ta Libiya.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Libiya ta fitar da rahoton cewa, a Shekara ta dubu biyu da sha bakawai da ta gabata an samu rahotonnin sace mutane da yawansu ya kai dubu da dari hudu a sassa daban daban na kasar.