IQNA

23:54 - September 07, 2018
Lambar Labari: 3482962
'Yan ta'addan takfiriyyah suna ci gaba da tserewa daga lardin Idlib na kasar Syria, a daidai lokacin da rundunar sojin kasar ta Syria take shirin fara kaddamar da wani gagarumin farmaki a kansu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, sakamakon firgicin da 'yan ta'addan takfiriyya suka shiga a yankin Idlib na Syria da suke iko da shi, bayan da sojojin Syria suka sanar da cewa suna shirin kaddamar da farmaki kan 'yan ta'adda a lardin, hakan ya sanya 'yan ta'adda da dama arcewa.

Rahoton ya ce wasu daga cikin manyan kwamandojojin 'yan ta'addan sun tsere daga yankin tun cikin 'yan makonnin da suka gabata, da sunan sun tafi aikin hajji, kamar yadda kuma wasu suke ta samun hanyoyin da suke sulalewa suna komawa kasashensu kafin sojojin na Syria su fara kaddamar da hare-haren tsarkake yankin baki daya daga 'yan ta'adda.

3744593

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، syria ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: