IQNA

Qasemi: Dole Gwamnatin Iraki Ta Hukunta Wadanda Suka Kai Harin Kan Ofishin Iran

22:30 - September 08, 2018
Lambar Labari: 3482963
Bangaren kasa da kasa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya kirayi gwamnatin Iraki da ta hukunta wadanda suka kai hari kan ofishin Iran da ke Basara.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a  lokacin da yake asa tambayoyin manema labarai a yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi, ya bayyana harin da wasu mutane suka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke Basara da cewa lamari mai matukar hadari.

Ya ce babbar manufar hakan ita ce rusa kyakkayawa alakar da ke tsaanin Iran da Iraki, wanda kuma hakan babu wanda zai amfanar sai makiya al’ummomin kasashen na Iran da Iraki.

Qasemi ya ce kai hari kan ofishin Iran a Basara ko alama abu ne da za a lamunta da shi ba, a kan ya ce dole ne gwamnatin Iraki ta dauki matakin gano wadanda suke da hannu a cikin lamarin domin hukunta su, kuma wajibi ne da ya rataya kan gwamnatin ta Iraki ta bayar da kariya ga jam’an diflomasiyya na Iran da kuma sauran wurare na diflomasiyyar Iran da ke cikin Iraki.

3744728

 

 

 

captcha