IQNA

22:33 - September 08, 2018
Lambar Labari: 3482964
Bangaren kasa da , an rubuta wani kwafin kur’ani mai tsari ami tsawon mita 16 a garin Faisal Abad na kasar Pakistan.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Imtiyaz Haidar wani mutum ne mai fasahar rubutu, wanda kuma shi ne ya rubuta wani kwafin kur’ani mai tsari ami tsawon mita 16 da hannunsa.

Ya ce tsawon kur’anin ya kai mita kusan 16 yayin da fadisa kuma ya kai mita 2.5, kuma an baje kolin kur’anin domin jama’a su duba.

Haka nan kuma Imtiyaz Haidar ya bayyana manufarsa ta rubuta wannan kur’ani da cewa, ita ce kara jawo hankulan jama’ar kasar domin su mayar da hankali ga lamarin kur’ani mai tsarki.

Nauyin wannan kur’ani dai ya kai kimanin kilogram 32.

3744803

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: