IQNA

22:38 - September 08, 2018
Lambar Labari: 3482966
Bangaren kasa da kasa, wasu masu dauke da makamai sun kaddamar da hare-hare a cikin jahar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, da yammacin yau Asabar wasu masu dauke da makamai sun kaddamar da hare-hare a kauyen Godumbali da ke jahar Borno.

Rahoton ya ce bisa ga bayanan da aka samu ‘yan bindigar sun kashe wasu daga cikin mutanen gari, kamar yadda kuma suka kasha wasu daga cikin jami’an sojin Najeriya.

‘Yan bindigar dai sun yi amfani da Babura ne da kuma motocin akori kura wadanda aka dora ma manyan bindigogi wajen kaddamar da harin, duk da cewa babu cikakken bayani daga jami’an tsaro kan harin da kuma adadin mutanen da suka rasa rayukansu.

 

3745055

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: