IQNA

23:49 - September 11, 2018
Lambar Labari: 3482973
Bangaren kasa da kasa, an dora tutocin makokin shahadar Imam Hussain (AS) a hubbarorin limaman shiriya na iyalan gidan manzo (SAW) a Iraki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Alkafil cewa, kamar kowace shekara a kasar Iraki an dora tutocin makokin shahadar Imam Hussain (AS) a hubbarorin limaman shiriya na iyalan gidan manzo (SAW) a lokacin da ake shirin fara tarukan ashura.

An fara gudanar da wannan aiki ne tun a daren jiya Litinin, da hakan ya hada da hubbaren Imam Hussain (AS) da kuma hubbaren Abbas (AS) da suke a birnin Karbala.

Sai kuma a birnin Najaf an dora wadannan tutocia  kan hubbaren Imam Amirul Mumimin (AS).

Masu jawabi kan waki’ar Karbala za su fara gudanar da jawabansu a wadannan wurare masu alfarma a cikin wadannan kwanaki na watan muharram.

3745840

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iraki ، hubbarori ، imam hussain ، Najaf
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: