IQNA

Abin Da Ke Faruwa A Khan Ahmar Shi Ne Hakikanin Mulkin Wariya

22:17 - September 14, 2018
Lambar Labari: 3482981
Daruruwan yahudawan sahyuniya sun kai farmaki kan kauyen Khan Ahmar da ke gabashin birnin Quds a yau Juma'a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau da rana tsaka daruruwan yahudawan sahyuniya sun kai farmaki kan kauyen Khan Ahmar da ke gabashin birnin Quds, inda suka yi ta lakada ma Falastinawa duka da cin zarafinsu, kamar yadda suka farfasa motocon daukar marassa lafiya da kuma kayan aikin 'yan jarida suka taru a wurin, wanda hakan ya zo ne kwanaki biyu bayan rusa gidajen Falastinawa da suke a wurin, inda Isra'ila ke shirin gina wasu sabbin matsagunnan yaudawa 'yan share wuri zauna.

Shugaban mabiya addinin kirista na darikar Arthodox a birnin Quds Ata'allah Hanna,a lokacin da yake zantawa da wata tawagar mambobin majalisar kungiyar tarayyar turai da suka ziyarce shi a yau, ya bayyana abin da ya faru a Khan Ahmar da cewa, shi ne hakikanin nuna wariya da kokarin kawar da wata al'ummar daga samu a cikin kasarta.

Ya ce kowa dai ya ga abin da yahudawan Isra'ila suke aikatawa kan al'ummar Palastine da wurare masu tsarki na musulmi da kirista da suke cikin birnin Quds da kewaye, da kuma yadda suke kame dubban mutane suna azabtar da su ba tare da duniya ta ce uffan ba, wanda hakan a cewarsa babban abin kunya ne musamman ga kasashen da suke raya cewa suna kare hakkokin bil adama da dimukradiyya.

3746724

 

captcha