IQNA

Jami’oin Kasar Masar Na Gudanar Da Gasar hardar Kur’ani

23:47 - September 15, 2018
Lambar Labari: 3482987
Bangaren kasa da kasa, jami’oin kasar Masar suna gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki a tsakanin dalibansu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Aldastur ta bayar da rahoton cewa, a yau an gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki a tsakanin daliban jami’oin kasar Masar guda 20.

Wannan gasa wadda ake gudanarwa a karkashin sanya ido na ministan ma’aikatar kula da harkokin addini na kasar Masar, tana samun halartar dalibai mata da maza wadanda suka hardace kr’ani mai tsarki.

Baya ga hardar kur’ani, ana gudanar da gasr kuma a wasu bangarori da suka hada da tilawa da kuma sanin ilimin hukuncehukuncen karatun kur’ani mai tsaki wato tajwidi.

Daga cikin alkalan da suke yin akalanci a gasar awai malamai uku daga cibiyar Azhar da kuma ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar.

3747179

 

 

 

 

 

captcha