IQNA

Gwamnatin Afghanistan Ta Dauki Matakan Bayar Da Kariya Ga Masu Tarukan Ashura

23:34 - September 19, 2018
Lambar Labari: 3482995
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Afghanistan ta dauki kwarar matakai na tsaro domin bayar da kariya ga masu gudanar da tarukan Ashura.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, sakamakon hare-haren ta’addancin da makiya mazhabar ahlul bait (AS) suke kai wa kan tarukan Ashura a wurare daban-daban a kasa Afghanistan, wannan ya sanya a wannan shekara gwamnatin kasar ta dauki kwarar matakai na tsaro domin bayar da kariya ga masu gudanar da wadannan taruka.

A cikin shekarun baya-bayan nan tun daga lokacin kafa kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi da suke kashe muuslmi a kasashe daban-daban da sunan jihadi, irin wadannan ‘yan ta’adda masu dauke da akidar wahabiyanci sun sha kai hare-haren bama-bamai a kan masallatai da cibiyoyin addini a lokacin da mabiya mazhabar shi’ar ahlul bait suke gudanar da tarukansu musamman ma na Ashura.

A wannan karon an tura daruruwa jai’an tsar da kayan aiki a dukkanin warren da ae gudana da arukan ashura a kasar Afghanistan, domin hana ‘yan ta’adda kai musu hare-hare.

3748389

 

 

 

 

captcha