IQNA

Iran Ta Yi Nasara / Trump Kuma ya Zama Saniyar Ware A Taron UN

9:05 - September 29, 2018
Lambar Labari: 3483018
Bangaren kasa da kasa, tun bayan da aka fara gudanar da babban taron zauren majalisar dinkin duniya a ranar Talata da ta gabata, daya daga cikin muhimman abubuwan da suka fi daukar hankali a taron shi ne kalaman kiyayya da Trump ya yi a kan kasar Iran, da kuma irin martanin da shugaba Rauhani na kasar Iran ya mayar masa.

Kamfanin dilalncin labaran IQNA, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban babban taron majalisar dinkin duniya karo na 73, shugaban Amurka Donald Trump ya yi dirar mikiya a kasar Iran, tare da jaddada cewa Amurka za ta ci gaba da kara matsa lamba kan Iran ta hanyar kakaba mata takunkumai, da kuma mayar da ita saniyar ware a duniya, tare da kiran kasashen duniya da su mara masa baya kan hakan.

Bayan jawabin na Trump ba da jimawa ba, shugaba Rauhani na Iran ya gabatar da nasa jawabin, inda ya mayarwa Donald Trump da martani, inda yake bayyana kalaman na Trump da cewa maimaci ne a kan dukkanin abubuwan da ya fada a baya, inda ya ce; ko shakka babu kalaman na Trump babbar barazana ce ga dokoki da ka'idoji na kasa, ta yadda Amurka za ta iya sanya kafa ta yi fatali da dokar majalisar dinkin duniya, kuma ta yi gaban kanta.

Rouhani ya ce ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya kan shirin Iran, wadda duniya ta amince da ita, hakan yana a matsayin keta hurumi ne na majalisar dinkin duniya wadda ta fitar da kudiri kan wannan yarjejeniya mai lamba 2232, wanda hakan ya mayar da yarjejeniyar ta zama ta duniya a hukumance, haka nan kuma wannan matsaya ta Amurka ta tozarta hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, wadda ta fitar da rahotanni har sau 12, da ke tabbatar da cewa Iran ba ta saba wa ko daya daga cikin abubuwan da aka cimma yarjejeniya a kansu ba.

To sai dai ga dukkanin alamu kiran na Donald Trump ga sauran kasashen duniya na su mara masa baya wajen takura ma kasar Iran tare da mayar da ita saniyar ware bai samu karbuwa ba, domin kuwa babu wata kasa da ta goyi bayansa kan hakan sai Saudiyya da Isra'ila, yayin da dukkanin kasashen kungiyar tarayyar turai gami da Birtaniya, da kuma sauran manyan kasashen duniya da suka hada da Rasha, China, Japan, Brazil , Malayzia, India Pakistan da sauransu, suka nuna cikakken goyon bayansu ga Iran, da kuma yarjejeniyar da aka cimmawa tare da ita.

Baya ga jawabin da Trump ya gabatar a gaban babban zauren majalisar dinkin duniya, bai tsaya anan ba, domin kuwa ya kirayi wani zaman taron na daban a kwamitin tsaron majalisar, inda a can ma ya sake maimaita kalaman nasa dangane da Iran, amma a nan take mambobin din-din-din na kwamitin tsaro suka mayar masa da martani kuma suka yi watsi da kamalan nasa.

Shugabannin kasashen duniya sun yi ta ganawa da shugaba Rauhani daya bayan daya a gefen taron, daga ciki kuwa har da shugaban Faransa Emmanuel Macron, Firayi ministar Birtaniya Theresa May, da kuam shugabannin kasashen turai daban-daban gami da na latin Amurka da Asia da Afrika.

Masana da dama kan harkokin siyasar kasa da kasa na ganin cewa, Amurka ta so ta yi amfani da babban taron na babban zauren majalisar dinkin duniya domin samun goyon bayan kasashen duniya wajen mayar da kasar Iran saniyar ware, amma kuma sai reshe ya juye da mujiya, inda Trump shi ne ya zama saniyar ware, saboda rashin samun goyon bayan kasashen duniya, yayin da shi kuma Rauhani aka yi ta rafsa masa tabi a bakin dayan zauren majalisar dinkin duniya, wanda hakan a zahiri yake nuni da cewa abin da Amurka ta shirya kan Iran a wurin taron bai yi nasara ba.

3750724

 

 

captcha