IQNA

Taron Cibiyoyin Kur’ani Na Afrika A Uganda

23:55 - October 20, 2018
Lambar Labari: 3483058
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taro na cibiyoyin kur’ani na kasashen Afrika a kasar Uganda.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ana shirin gudanar da zaman taro na cibiyoyin kur’ani na kasashen Afrika a kasar Uganda, wanda cibiyar yada al’adu da harkokin ilimi ta kasashen musulmi ISESCO za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.

Wannan taro dai zai mayar da hankali kan hanyoyin bunkasa makarantun kur’ani da kuma hanyoyin koyarwa na zamani a kasashen Afrika, musamman ma wadanda ba su da karfin tattalin arziki.

Taron zai samu halartar malamai da wakilan cibiyoyin ilimi da makarantu daban-daban na addini daga kasashen Afrika, inda za a gabatar da shawarwari kan hanyoyin bunkasa ilimin kur’ania  nahiyar Afrika.

Kasar Ugadanda da ke gabashin nahiyar Afrika tana da adadin mutane da ya kai miliyan 37, kuma kimanin miliyan 12 daga cikinsu mabiya addinin muslunci ne.

3757227

 

 

 

 

captcha