IQNA

Martanin Iran Kan Takunkumin Amurka

23:52 - November 05, 2018
Lambar Labari: 3483102
Bnagaren kasa da kasa, Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bada sanarwan cewa shirin musayar kudade tsakanin Iran da kasashen tarayyar Turai na tafiya kamar yadda ya dace

Kamfanin dillancin labaran iqna, Bahram Qasem,i kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ne ya bayyana haka a yau litinin, a lokacinda yake bayani wa kafafen yada labarai na ciki da wajen kasar.

Qasemi ya kara da cewa shirin musayar kudaden yana da muhimmanci, musamman bayan da Amurka ta dawo da takunkuman da ta dorawa kasar Iran na hanta sayar da danyen man fetur na kasar. 

Dangane da dawo da takunkumin kuma, Qasemi ya ce Amurka ce ta dorawa kanta takunkumi, don abinda ta yi ya sabawa dokokin kasa da kasa, banda haka kasashen duniya da dama basu amince da matakin da ta dauka ba. Har'ila yau bada izini ga wasu kasashe su ci gaba da sayan man fetur na kasar Iran , wanda gwamnatin Amurka ta yi, jada baya ne daga takunkumin.

takunkumin na Amurka dai na zuwa ne 'yan watanni bayan ficewar Donald Trump daga yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran da sauran manyan kasashen duniya.

Babu wata kasa daga cikin kasashen da suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya da ta amince da wannan mataki da Amurka ta dauka.

Kasar Iran ta bayyana matakin na Amurka da cewa ya kara fito da matsayin gwamnatin Amurka a fili ne, kan cewa ita ce take karya ka'idoji da yarjeniyoyi na kasa da kasa.

Iran dai ta ce za ta ci gaba da mutunta wannan yarjejeniyar matukar dai sauran bangarorin da suke cikin yarjejeniyar suna ci gaba da mutunta ta, ko da kuwa ba tare da Amurka ba.

 

3761549

 

 

 

captcha