Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bawwaba Alahram cewa, a jiya ne aka bude babbar gasar kur’ani mai tsarki ta mata zalla a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa tare da halartar wakilan kasashen duniya.
Bayan bude taron gasar ta kasa da kasa akaro na uku, masu gasa 6 ne suka fara karawa da juna daga kasashen Kamaru, Belgium, Philipines, Saudiyya, Iraki da Afrika ta kudu.
Kasashe 63 ne suke halartar gasar wadda aka fara daga 4 zuwa 16 na watan fabrairu.