IQNA

Shugabannin Kasashe 60 Za Su Halarci Zaman Sulhu A Paris

23:55 - November 06, 2018
Lambar Labari: 3483106
Bangaren kasa da kasa, shugabannin kasashe 60 ne za su halarci taron sulhu a birnin Paris na kasar Faransa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin Russia yaum ya bayar da rahoton cewa, Emmanuel Macron shugaban Faransa ya sheda cewa, shugabannin kasashe 60 ne aka ajiye magana da su wadanda za su halarci taron sulhu a birnin Paris da a za a gudanar.

Wannan taro dai ana gudanar da shi ne duk shekara-shekara domin tunawa da kawo karshen yakin duniya na farko, wanda kuma wannan shi ne karo na dari da za a gudanar da taron, wanda zai samu halartar shugabannin kasashe da uka hada Vladimir Putin na Rasha, Trump na Amurka, da firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Shugabannin kasashen za su gana da juna a gefen taron.

3761705

 

 

 

 

 

captcha