IQNA

Jam'iyyar Democrat ta Samu Rinjaye A Majalisar Wakilan Amurka

22:56 - November 07, 2018
Lambar Labari: 3483110
Jam'iyyar Democrats ta Amurka ta yi nasara a zaben rabin wa'adin zango bayan da ta doke jam'iyyar Republican a majalisar wakilan kasar, lamarin da ake ganinsa a matsayin gagarumin koma baya ga shugaban kasar Donald Trump.

Kamfanin dillancin labaran iqna, sakamakon zaben yana nuni da cewa jam'iyyar Democrats din ta 'yan adawa ta sami kujeru dari biyu da sha takwas a majalisar a yayin da ita kuma jam'iyyar Repulican ta samu kujeru dari da casa'in da uku.

Sai dai a bangaren majalisar dattawan kasar kan jam'iyyar Republicans da ke da rinjaye a majalisar dattawa na kan hanyarta ta ci gaba da rike rinjayen da take da shi a majalisar da kujeru  hamsin da daya yayin da Democrats ke da arba'in da tara a zauren majalisar.

Duk da cewa 'yan Republican din suna da rinjaye a majalisar dattawan wanda hakan zai iya ba wa shugaba Trump din damar zartar da kudurce-kudurcensa, to amma duk da hakan rasa majalisar wakilan da jam'iyyar Republican din ta yi da kuma yadda wasu 'yan jam'iyyar Republican din suke nuna adawa da wasu siyasarsa, hakan zai ci gaba da zama masa wani karfen kafa wajen aiwatar da abin da yake so.

3762099

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha