IQNA

Belgium Ta Kara Daga Wakilcin Diflomasiyyar Palastine A Kasarta

20:42 - November 09, 2018
Lambar Labari: 3483116
Bangaren kasa da kasa, Belgium ta sanar da cewa ta kara daga wakilcin diflomasiyyar Palastine a kasarta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Didier Reynders ministan harkokin wajen kasar Belgium, bayan wata ganawa da ya yi da takwaransa na Palastine Riyad Maliki ya bayyana cewa, kasarsa ta kara daga wakilcin diflomasiyyar Palastine.

Ya ce wannan mataki na zuwa ne bayan gudanar da wata tattaunawa tare da manyan jami'ai na majlaisar dinkin duniya, ta yadda a halin yanzu Palastinu za ta kara yawan jami'an diflomasiyyarta, kuma za su samu wasu Karin abubuwan da ba su da su a lokutan baya ta fuskar diflomasiyya.

Abdulkarim Alfarra wakilin Palastine a kasar Belgium ya bayyana cewa,a  halin yanzu kasar ta Belgium ta dauki matakin bayar da dama ga Palastine da ta turo jakada maimakon wakili, kuma ta bude ofishin jakadanci maimakon ofishin wakilci.

3762348

 

captcha