IQNA

Za A Bude Wani Asusun Ajiya Na Musulmi A Kasar Kenya

21:46 - November 10, 2018
Lambar Labari: 3483119
Musulmin kasar Kenya na shirin bude wani tsari na asusun ajiya ga wadanda suka yi ritaya daga ayyukansu.

Shafin yada labarai na Abro ya bayar da rahoton cewa, mabiya addinin musulunci a kasar Kenya sun fito da wani shiri na samar da tsarin asusun ajiya ga musulmi wadanda suka yi ritaya daga ayyukansu.

Tsarin ajiyar dai zai kasance ne daidai da ka'idoji irin na addinin muslunci, ta yadda masu ajiyar za su amfana daga abin da suka ajiye bisa tsarin da aka yi.

Haka nan kuma rahoton ya ce hatta wadanda ba musulmi ba za su iya amfana da wannan tsari, da sharadin kiyaye ka'idojin da aka gindaya wadanda suka yi daidai da tsarin ajiya a musulunci.

Baya ga haka kuma za a yi amfani da kudaden wajen kasuwanci, amma ba za a yi amfani da su a cikin duk wani nau'in kasuwancin da riba ta shiga ciki ba, ko kasuwancin giya da sauran ababen da musulunci ya haramta.

3762561

 

 

 

 

captcha