IQNA

Jagora: Iran Na Bukatar Ganin Iraki Mai Karfi Da 'Yanci

23:03 - November 18, 2018
Lambar Labari: 3483132
A jiya ne shugaban kasar Iraki Barham Saleh ya gudanar da wata ziyarar aiki a kasar Iran, inda ya gana da mayan jami'an gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Bayan isowarsa birnin Tehran a jiya, ya samu tarba daga shugaban Iran, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma wajabcin ci gaba da kara fadada wannan alaka a dukkanin bangarori, da suka hada siyasa, tattalin arziki, cinikayya, al'adu da sauransu.

Shugabani ya bayyana cewa, kasashen Iran da Iraki sun kudiri aniyar ci gaba da yin aiki tare domin amfanin al'ummominsu, wanda kuma babu gudu babu ja da baya kan hakan.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Iraki Barham Saleh ya bayyana cewa, alaka tsakanin kasashen Iran da Iraki alaka ce ta tarihi, wadda babu wani abu da zai iya rusa ta, tare da jaddada cewa kasashen biyu suna bababn tasiri a yankin, wanda haan ya kara tabbatar da wajabcin yin aiki tare a tsakaninsu, domin ci gaban al'ummominsu da ma al'ummomin yankin baki daya.

An rattaba hannu tsakanin bangarorin biyu kan yarjeniyoyi da dama, musamman a bangarori na tattalin arziki da kasuwanci da karfin wutar lantarki gami da sufuri da kuma tsaro, inda shugaba Rauhani ya bayyana cewa, harkar kasuwanci tsakanin Iran da Iraki ya kai dala biliyan 12 a shekara, amma nan ba da jimawa ba za ta karu zuwa dala biliyan 20 a shekara.

Haka nan kuma an rattaba hannu tsakanin kamfanonin Iran da gwamnatin Iraki, kan gina layin dogo a cikin kasar Iraki, wanda zai hada yankunan kudu da arewa na kasar, domin saukaka harkokin sufuri, da kuma daukar kayayyakin kasuwanci zuwa bangarorin kasar, wanda kamfanonin Iran ne za su gudanar da wannan aikia  cikin kasar ta Iraki.

Bayan kammala ganawa ad shugaba Rauhani da kuma sanya hannu kan yarjeniyoyi tsakanin gwanatocin kasashen biyu, shugaba Barham Saleh tare da rakiyar shugaba Rauhani ya ziyarci jagoran juyin juya halin muslunci a Iran A yatollah Sayyid Ali Khamenei.

Jaoran ya jadda matsayin Iran na ci gaba da kasancewa tare da Iraki a kowane lokaci, tare da bayyana kasashen biyu na Iran da Iraki da cewa suna fuskantar babban kalu bale daga wasu 'yan tsirarun kasashe na yankin da kuam wasu wadanda ba na yankin ba, wadanda basa fatan ganin alkhairi a Iran ko Iraki, wanda kuma tare da jajircewar al'ummomin kasashen biyu, za su yi nasara wajen cimma burinsu da ci gaban al'ummominsu.

Shi ma  anasa bangaren shugaba Barham Sale ya yaba da irin rawar da Iran ta taka wajen taimaka kasar Iraki a bangarori daban-daban, musamman a bangaren tsaro, inda Iran ta bayar da dukkanin gudunmawa wajen murkushe 'yan ta'adda a Iraki, wanda a cewarsa wannan lamari ne da ya shiga cikin kundin tarihi da ba za a taba mantawa da shi ba.

Bayan nan kuma Saleh ya gana da wasu daga cikin manyan jami'an kasar ta Iran, da suka hada da ministan harkokin wajen kasar Dr. Muhamad Jawad zarif, sai kuma shugaban majalisar dokokin kasar Ali Larijani, da kuma shugaban majalisar tsaron kasa Ali Shamkhani, inda suka tattauna a kan batutuwa daban-daban da suk shafi bunkasa alaka tsakanin kasashen biyu.

Da dama daga ciin masana kan harkokin siyasar yankin sun yi imanin cewa, ko shakka babu, karfafa alaka tsakanin Iran da Iraki na da gagarumin tasiri ga makomar lamurra  a yankin gabas ta tsakiya, a siyance da kuma ta fuskar tsaro har ma da fuska ta tattalin arziki.

3764764

 

captcha