Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bada rahoton cewa, firayi ministan Australia Scott Jhon Morison ya sanar da cewa, kasar ta amince da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra’ila.
Ya ci gaba da cewa, duk da cewa kasarsa ta amince da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra'ila, amma kuma a halin yanzu ba su da wani shiri na dauke ofishin jakadancinsu daga Tel aviv zuwa birnin na Quds.
Kasar Australia dai na daga cikin kasashe masu bin siyasar Amurka ido rufe, kuma wannan matakin na zuwa ne bayan da gwamnatin Amurka karkashin shugabancin Donald Trump ta fara amincewa da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra'ila, tare da dauke ofishin jakadancinta daga Tel aviv zuwa birnin Quds, lamarin da kasashen duniya suka yi Allawadai da shi, da hakan ya hada har da kasashen yammacin turai masu kawance da Amurka.