IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Quds A Istanbul Ya Yi Watsi Da Yarjejeniyar Karni

22:12 - December 16, 2018
Lambar Labari: 3483222
Bangaren kasa da kasa, babban taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Istanbul na kasar Turkiya kan bbatun Quds ya yi watsi da yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, an kammala zaman taron ‘yan majalisar dokoki daga kasashen duniya kan batun Quds a birnin Istanbul, kuma bayanin bayan taron ya tir da Allawadai da abin da ake kira yarjejeniyar karni.

Wannan taro dai kwamitin ‘yan majalisar dokokin kasashen musulmi da ke karkashin kungiyar kasashen muuslmi ta OIC ne ya dauki nauyin shirya, duk kuwa da cewa an gayyaci sauran majalisa daga kasashen duniya daban-daban har da wadanda ba na kasashen musulmi a wurin taron.

Babban abin da bayanin bayan taron ya fi mayar da hankali a kansa shi ne shi ne wajabcin taka wa Isra’ila birki kan cin zalun da take yi wa Falastinawa, tare da kawo karshen mamyar yankunansu da take yi musamman a birnin Quds da kuma yankunan gabar yamma da kogin Jordan.

Bayanin bayan taron ya kirayi hukumar UNESCO da taka taka rawa wajen kare wurare tarihi na Palastine da Isra’ila ke hankoron kawar da su, kamar yadda bayanin ya dora wannan nauyi a kan dukkanin kasashen duniya.

Taron ya yi Allawadai da abin da ake kira yarjejeniyar karni, wadda ke nufin mayar da birnin quds fadar mulkin gwamnatin yahudawan Isra’ila a hukumance, tare da haramtawa Falastinawa da Isra’ila ta kora dawowa kasarsu, wanda Amurka da wasu kasashen larabawa da suka hada Saudyiyya suke da nufin tabbatar da hakan a hukumance tare.

‘Yan majalisar dokoki 600 ne daga kasashe 74 na duniya suka halarci taron na Istanbul.

3772724

 

 

 

 

captcha