IQNA

Majalisar Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Gudanar Da Zaman Gaggawa Kan Palastine

23:56 - December 18, 2018
Lambar Labari: 3483228
Bangaren kasa da kasa, majalisar kungiyar kasashen larabawa ta gudanar da zaman gaggawa a yau dangane da batun Palastine.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wakilan din-din-din na kasashen larabawa a malaisar kungiyar kasashen larabawan suke gudanar da zamana  yau a birnin Alkahira na kasar Masar.

A lokacin taron Said Abu Ali mataimakin babban sakataren kungiyar ya gabatar da jawabinsa, inda ya bayyana batun Palastine shi ne farko kuma mafi muhimmanci ga dukkanin al’ummomin larabawa.

Shi ma a nasa bangaren Rayad Maliki ministan harkokin wajen Papastine ya gabatar da nasa jawabin, inda su ne suka bukaci da a gudanar da wannan za,a na gaggawa, bisa la’akari da halin da ake ciki, inda Isra’ila ke ta kara matsa lamba wajen cutar da al’ummar Palastine.

Wannan dai na zuwa ne  a lokacin da ake sa ran kasar Brazil za ta amince da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra’ila a hukumance, ‘yan kwanaki bayan Australia ta sanar da amincewa da Quds ta yamma a matsayin babban birnin Isra’ila.

3773689

 

 

 

 

 

captcha