IQNA

23:47 - December 22, 2018
1
Lambar Labari: 3483241
Rundunar sojojin kasar Myanmar ta sanar da dakatar da bude wuta kan yankunan musulmin Rohingya har tsawon watanni hudu masu zuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, ofishin bababn hafsan hafsoshin rundunar sojin  kasar ta Myanmar ne ya sanar da hakan a jiya Juma'a, a wani mataki na neman ganin an shiga tattaunawa da musulmin.

bayanin ya ce wannan matakin daga bangaren sojoji ne, kuma za su bayar da dama daga nan har zuwa 30 ga watan Afirilun 2019 ga musulmi 'yan aware da su sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta.

Wannan dai shi ne karon farko da rundunar sojin kasar Myanmar ta taba sanar da dakatar da bude wuta daga bangarenta kan musulmin Rohingya a cikin shekaru fiye da talatin da take kaddamar da farmakin sojia  kansu lokaci zuwa lokaci.

Myanmar dai na fuskantar babban matsain lamba daga kasashen duniya, dangane da kisan kiyashin da sojojin kasar da kuma 'yan addini buda masu tsatsauran ra'ayi suka yi kan musulmi daga shekara ta 2015 ya zuwa yanzu.

3774356

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، musulmi ، shekara ، addini
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 1
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Allah katemaki musulinci da musulmi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: