Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Mayakan kungiyar 'yan ta'adda ta Al-shabab ta kaddamar da hare-hare da makaman roka a kan babban sansanin majalisar dinin duniya a kasar Somalia, wanda yake a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Somalia Nicholas Haysom ya bayyana cewa, an kai harin ne a kan bababn ofishin na majalisar dinkin duniya da makaman roka, wanda hakan a cewarsa babban abin bakin ciki ne, domin aikinsu a Somalia shi ne taimaka ma al'ummar kasar.
Ya ce suna yin Allah wadai da wannan hari a kan babban sansanin majalisar dinkin duniya a kasar Somalia, kuma suna fatan kasashen duniya za su dauki matakin kare dukkanin wurare na majalisar duniya da suke a cikin kasar.
Kungiyar Al-shabab ta sanar da cewa ita ce take alhakin kai wannan hari, wanda ya jikakta ma'aikatan majalisar dinkin duniya uku, da kuma yin barna ta kaddarori a wurin.