IQNA

Isra’ila Ta Fita Daga Hukumar UNESCO

23:51 - January 03, 2019
Lambar Labari: 3483279
Bangaren kasa da kasa, Isra’ila ta sanar da ficewa daga hukumar raya ilimi da al’adu da kuma tarihi ta majalisar dinkin duniya wato UNESCO.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a  cikin wani rahoto da shafin jaridar Arabi 21 ya buga, ya bayyana cewa Isra’ila ta sanar a hukumance cewa ta fice daga cikin mambobin UNESCO.

Wannan mataki na Isra’ila da I ya zo ne bayan ficewa Amurka, bisa hujjar cewa hukumar ta UNESCO tana goyon bayan Falastinawa, tare da kin amincewa da wuraren tarihi a Palastine da Isra’ila take danganta kanta da su, inda hukumar take tabbatar da cewa suna da alaka da al’ummar falastine ne.

Jakadan Isra’ila a majalisar dinkin duniya Dani Danon ya bayyana cewa, hukumar UBESCO taki amincewa da cewa birnin Quds mallakin Isra’ila ne, inda ta tsaya kai da fata a kan cewa birnin na Falastinawa ne, kamar yadda kwamitin bincike na UNESCO ya gabatar da hakan.

Wannan kuwa ya zo a cikin sakamakon binciken da kwamitin ya bayarne kan wannan batu tun a cikin watan Yukin 2017, inda kuma a kan hakan ne hukumar ta fitar da sakamakon binciken da ke tabbatar da cewa birnin Quds na Falastinawa ne, lamarin da ya bakanta ran Amurka da Isra’ila, kuma suka fice daga cikin hukumar bisa wannan dalili.

3777693

 

 

 

captcha