IQNA

Albashir: An Ba Mu Shawara Da Mu Kulla Alaka Da Isra'ila

23:21 - January 05, 2019
Lambar Labari: 3483286
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya bayyana cewa, an ba su shawara da su kulla alaka da Isra'ila domin lamurran kasar Sudan su kyautata.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya bayyana cewa, an ba su shawara da su kulla alaka da Isra'ila domin su samu saukin matsalolin tattalin arziki da kasarsu ke fama da su.

Albashir wanda yaki fadin kasashen da suka ba shi wannan shawara, amma dai ya bayyana cewa; arziki na hannun Allah ne, kuma Sudan ba za ta daina goyon bayan Palastin e ba.

Tun kafin wannan lokacin dai 'yan adawa  akasar ta Sudan sun zargi Albashir da yankurin kulla alaka da Isra'ila, lamarin da akasarin mutanen kasar suka nuna rashin amincewa  akansa.Yanzu haka dai Sudan na fama da matsaloli na tattalin arziki masu tarin yawa, duk kuwa da irin alkawullan da Saudiyya ta yi wa kasar ta Sudan idan har ta amince ta shiga yakin da Saudiyya ke jagoranta kan al'ummar kasar Yemen, inda shekaru uku kenan sojojin gwamnatin Sudan suna yi wa Saudiyya yaki a Yemen a matsayin sojojin haya, amma har yanzu Saudiyya ba ta yi wa kasar da Sudan komai ba ta fuskar tattalin arziki.

Kimanin makonni uku kenan al'ummar Sudan suna gudanar da zanga-zanga kan abin da suka kira gazawar gwamnatin Albashir wajen kayutata rayuwar jama'a, inda a yanzu suke yin kira da ya sauka domin a  kafa gwamnatin rikon kwarya.

Tun shekara ta 1989 Albashir ke mulki a kasar Sudan, bayan da ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin kasar a lokacin.

3778250

 

 

 

captcha