IQNA

An Kame Malamn Jami’a 14 A Kasar Sudan

21:09 - January 06, 2019
Lambar Labari: 3483289
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaro sun kame malaman jami’ar Khartum 14 saboda nuna goyon baya ga masu zanga-zanagar adawa da siyasar Albashir.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamafanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, a yau Asabar daruruwan masu zanga-zanga ne suka taru a gaban jami’an Khartum, da suka hada da dalibai da kuma mutanen gari, inda wasu malaman jami’a suka shiga cikin masu gangamin.

Rahoton y ace jami’an tsaro sun kame 14 daga malaman jami’ar a lokacin da suke fitowa da nufin shiga zanga-zangar, kamar yadda kuma jami’an tsaro suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu gangamin a lokacin da suka nufi hanyar da isa fadar shugaban kasar a cikin birnin Khartum.

Tun fiye da makonni uku da suka gabata ne al’ummar Sudan suka fara bore kan matsaloli na tattalin arziki da suka addabi kasar, inda yanzu kuma zanga-zangar ta koma neman Albashir ya sauka daga kan mulkin bayan da ya share shekaru talatin a kan kujerar shugabancin Sudan.

Gwamnati ta ce ya zuwa yanzu mtane sha tara suka mutu, amma kungiyoyin farar hula sun ce mutanen da jami’an tsaro suka kasha ya zuwa a cikin zanga-zangar sun kai talatin da bakwai.

3778977

 

 

 

 

captcha